Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 4:43 - Littafi Mai Tsarki

43 Biranen su ne, Bezer cikin jeji a kan tudu domin Ra'ubainawa, da Ramot cikin Gileyad domin Gadawa, da Golan cikin Bashan domin Manassawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

43 Biranen kuwa su ne, Bezer a dutsen hamada, don mutanen Ruben; Ramot Gileyad, don mutanen Gad; da kuma Golan a Bashan, don mutanen Manasse.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 4:43
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A hayin Urdun, gabas da Yariko, suka keɓe Bezer ta jeji a kan tudu a cikin yankin kabilar Ra'ubainu, da Ramot cikin Gileyad ta kabilar Gad, da Golan cikin Bashan ta kabilar Manassa.


Daga na kabilar Gad kuma an ba da Ramot ta Gileyad duk da makiyayarta, da Mahanayim duk da makiyayarta,


Daga na rabin kabilar Manassa na gabas, an ba 'ya'yan Gershon, maza, Golan ta Bashan tare da makiyayarta, da Ashtarot duk da makiyayarta.


Daga cikin kabilar Gad aka ba su birane huɗu, su ne Ramot ta Gileyad da wuraren kiwo nata, wannan birnin mafaka ne domin wanda ya yi kisankai, da Mahanayim da wuraren kiwo nata, da Heshbon da wuraren kiwo nata, da Yazar da wuraren kiwo nata.


Aka ba iyalan Gershonawa na cikin Lawiyawa birane biyu daga cikin rabo na rabin kabilar Manassa. Biranen su ne, Golan tare da wuraren kiwo nata, cikin Bashan, ita kuwa birnin mafaka ce saboda wanda ya yi kisankai, da Ashtarot da wuraren kiwo nata.


domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can, wato wanda ya kashe mutum ba da niyya ba, babu kuma ƙiyayya tsakaninsu a dā. In ya gudu zuwa ɗaya daga cikin biranen zai tsirar da kansa.


Waɗannan su ne dokokin da Musa ya ba Isra'ilawa,


Aka kuma ba su birane huɗu daga cikin rabon kabilar Ra'ubainu. Biranen ke nan, Bezer da wuraren kiwo nata, da Yahaza da wuraren kiwo nata da Kedemot da wuraren kiwo nata, da Mefayat da wuraren kiwo nata.,


Haka kuma aka ba 'ya'yan Merari, maza, bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga na kabilar Ra'ubainu, da na kabilar Gad, da na kabilar Zabaluna.


Waɗansu daga cikin iyalan 'ya'yan Kohat, maza, sun sami garuruwa na yankinsu daga cikin kabilar Ifraimu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ