Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 4:33 - Littafi Mai Tsarki

33 Akwai wata jama'a da ta taɓa jin muryar wani allah tana magana ta tsakiyar wuta kamar yadda kuka ji, har suka rayu?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

33 Akwai waɗansu mutanen da suka taɓa jin muryar Allah yana magana daga wuta, kamar yadda kuka ji har suka rayu?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 4:33
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da Gidiyon ya gane mala'ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Kaitona, Ubangiji Allah, gama na ga mala'ikan Ubangiji fuska da fuska.”


suka ce, ‘Ga shi, Ubangiji Allahnmu ya bayyana mana ɗaukakarsa da girmansa, mun kuma ji muryarsa a tsakiyar wutar. Yau mun ga Allah ya yi magana da mutum, duk da haka ya rayu.


Ya kuma ce, “Ba za ka iya ganin fuskata ba, gama mutum ba zai gan ni ba, ya rayu.”


Akwai wani ɗan adam wanda ya taɓa jin muryar Allah, Allah Mai Rai yana magana ta tsakiyar wuta yadda muka ji, har ya rayu?


Amma Ubangiji bai yi wa dattawan Isra'ila wani abu ba, ko da yake suka ga zatin Allah. Su kuma suka ci suka sha a gaban Allah.


Ubangiji kuwa ya ba ni allunan nan biyu na dutse da shi kansa ya rubuta. A kansu aka rubuta maganar da Ubangiji ya yi muku daga bisa dutsen a tsakiyar wuta a ranar taron.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Haka za ka faɗa wa Isra'ilawa, ‘Ku da kanku kun ji na yi magana da ku daga sama.


Ya sa ku ji muryarsa daga Sama don ya horar da ku. Ya kuma sa ku ga babbar wutarsa a duniya, kuka kuma ji muryarsa daga cikin wutar.


Ubangiji ya yi muku magana fuska da fuska bisa dutsen ta tsakiyar wuta.


“Ubangiji ya faɗa wa taron jama'arku waɗannan dokoki da murya mai ƙarfi ta tsakiyar wuta, da girgije, da duhu baƙi ƙirin. Ya rubuta su a bisa alluna biyu na dutse, ya ba ni, ba abin da ya ƙara.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ