M.Sh 4:31 - Littafi Mai Tsarki31 Ubangiji Allahnku, Allah mai jinƙai ne. Faufau, ba zai kunyata ku ba, ba kuwa zai hallaka ku ba, ba kuma zai manta da alkawarin da ya rantse wa kakanninku ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202031 Gama Ubangiji Allahnku, Allah ne mai jinƙai; ba zai yashe ku ko yă hallaka, ko kuma yă manta da alkawarin da ya yi da kakanninku, wanda ya tabbatar da su da rantsuwa ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.