Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 4:25 - Littafi Mai Tsarki

25 “Sa'ad da kuka haifi 'ya'ya, kuka sami jikoki, kuka kuma daɗe cikin ƙasar, idan kuka yi abin da yake haram, wato kuka yi gunki na sassaƙa na kowace irin siffa, kuka kuma aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku har kuka tsokane shi ya yi fushi,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Bayan kun haifi ’ya’ya da jikoki, kuka kuma zauna na dogon lokaci a ƙasar, in har kuka lalace, kuka kuma yi wani irin gunki, kuna aikata mugunta a gaban Ubangiji Allahnku, kuna kuma sa shi fushi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 4:25
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,


Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?


Sun yi zurfi cikin rashin gaskiya Kamar a kwanakin Gibeya, Ubangiji zai tuna da muguntarsu. Zai hukunta su saboda zunubansu.


Ya aikata mugun abu a gaban Ubangiji, gama ya aikata abubuwa masu banƙyama waɗanda al'umman da Ubangiji ya kora a gaban jama'ar Isra'ila suka aikata.


Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama jama'arka da ka fito da su daga ƙasar Masar sun ƙazantar da kansu.


Saboda haka, ku lura fa, kada ku manta da alkawarin da Ubangiji Allahnku ya yi da ku, don haka kada ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane irin kamanni wanda Ubangiji Allahnku ya hana ku.


“Dukan waɗannan la'anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba.


Har yanzu kuma Ubangiji zai kawo muku kowace irin cuta, da kowace irin annoba, waɗanda ba a ambace su a littafin dokokin nan ba, har ku hallaka.


Sun aikata mugunta a gabansa, Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu, Su muguwar tsara ce, karkatacciya,


Lokacin da kuka karya alkawarin Ubangiji Allahnku da ya umarce ku, kuka tafi kuka bauta wa gumaka, kuka sunkuya musu, to, Ubangiji zai yi fushi da ku, zai kuwa hallaka ku daga ƙasa mai albarka da aka ba ku.”


Idan kun rabu da Ubangiji, kun bauta wa gumaka, sai ya juyo ya wulakanta ku, ya hallaka ku, ko da yake ya riga ya nuna muku alheri.”


Suka sa shi ya yi fushi saboda Masujadansu na arnanci. Suka sa ya ji kishi saboda gumakansu.


“Kada ka yi wa kanka wani gunki ko kuwa wata siffa ta wani abu a sama a bisa, ko a duniya a ƙasa, ko kuma a ruwa a ƙarƙarshin ƙasa.


Kada kuma ku kafa al'amudi, abin da Ubangiji Allahnku yake ƙi.”


“ ‘La'ananne ne mutumin da ya sassaƙa, ko ya ƙera gumaka, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannun mai sana'a, ya kafa ta a ɓoye.’ “Sai dukan jama'a su amsa, ‘Amin, Amin!’


to, ina faɗa muku yau, lalle za ku hallaka. Ba za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun ku shiga ciki don ku mallake ta ba.


Ina kiran sama da duniya su zama shaidu a kanku yau, cewa na sa rai da mutuwa a gabanku, da albarka da la'ana. Ku zaɓi rai fa, don ku rayu, ku da zuriyarku.


Da na shiga, sai na ga zānen siffofin kowane irin abu mai rarrafe, da haramtattun dabbobi, da dukan gumakan mutanen Isra'ila kewaye da bangon.


Allahna zai ƙi su Domin ba su yi masa biyayya ba. Za su zama masu yawo cikin al'ummai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ