Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 4:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Amma Ubangiji ya yi fushi da ni sabili da ku, har ya rantse, cewa ba zan haye Urdun in shiga kyakkyawar ƙasan nan wadda yake ba ku abar gādo ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, ya kuma yi rantsuwa cewa ba zan haye Urdun, in shiga ƙasan nan mai kyau da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 4:21
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ma ya yi fushi da ni sabili da ku, ya ce, ‘Har kai ma ba za ka shiga ba.


Ubangiji kuwa ya ce wa Musa da Haruna, “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra'ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama'ar nan a ƙasar da na ba su ba.”


Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’


“Amma Ubangiji ya yi fushi da ni saboda ku, don haka bai ji ni ba. Ya ce mini, ‘Ya isa. Kada ma ka sāke yi mini magana a kan wannan al'amari.


Gama ba ku kai wurin hutawa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku gādo ba tukuna.


“Ba za a sami matalauci a cikinku ba, da yake Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, ku mallaka,


Sai ku shirya hanyoyi, ku kuma raba yankin ƙasa wanda Ubangiji Allahnku zai ba ku ku mallaka kashi uku, domin wanda ya yi kisankai ya gudu zuwa can.


don kada a zubar da jinin marar laifi a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo, domin kada alhakin jini ya kama ku.


“Amma kada ku bar kome da rai a garuruwan mutanen nan da Ubangiji Allahnku yake ba ku su gādo.


kada a bar gawarsa ta kwana a kan itacen. Sai ku binne shi a ranar da aka rataye shi, gama wanda aka rataye shi la'ananne ne ga Ubangiji. Ku binne shi don kada ku ƙazantar da ƙasar da Ubangiji Allah yake ba ku, ku gāda.”


to, kada mijinta na fari wanda ya sake ta, ya sāke aurenta, tun da yake ta ƙazantu. Gama wannan abar ƙyama ce a wurin Ubangiji. Kada ku jawo alhaki a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda.


“Sa'ad da kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku gāda, kuka mallake ta, kuka zauna cikinta,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ