M.Sh 4:19 - Littafi Mai Tsarki19 Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202019 Sa’ad da kuka ɗaga ido kuka kali sama, kuka ga rana da wata, da taurari, da dukan halittun sama, sai ku kula fa, kada ku jarrabtu, ku ce za ku yi musu sujada, ko ku bauta musu; abubuwan nan Ubangiji Allahnku ne ya rarraba wa dukan al’umman da suke ko’ina a ƙarƙashin sararin sama. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |