Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 33:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa, ‘Ban kula da ku ba.’ Ya ce wa 'yan'uwansa su ba nasa ba ne. Ya kuma ƙyale 'ya'yansa, Domin sun kiyaye maganarka, Sun riƙe alkawarinka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ya yi zancen mahaifinsa da mahaifiyarsa ya ce, ‘Ban kula da su ba.’ Bai gane da ’yan’uwansa ba, ko yă yarda da ’ya’yansa, amma ya kiyaye maganarka ya tsare alkawarinka.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 33:9
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da ubansa, da uwa tasa, da mata tasa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa mata da maza, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba.


Sai ya amsa wa wanda ya gaya masa, ya ce, “Wace ce tsohuwata, su wane ne kuma 'yan'uwana?”


Wanda duk ya fi son ubansa ko uwarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba. Wanda kuma ya fi son ɗansa ko 'yarsa fiye da ni, bai cancanci zama nawa ba.


To, wato ni son mutane nake nema ne, ko kuwa na Allah? Ko kuwa ƙoƙari nake yi in faranta wa mutane zuciya? Da har yanzu mutane nake faranta wa zuciya, ai, da ban zama bawan Almasihu ba.


Saboda haka, a nan gaba ba mā ƙara duban kowane mutum bisa ga ɗabi'ar jiki kawai, domin ko da yake mun taɓa duban Almasihu bisa ga ɗabi'ar jiki, yanzu ba ma ƙara dubansa haka.


Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.


Sa'an nan suka ce, “Zo mu shirya wa Irmiya maƙarƙashiya, gama firist ba zai bar bin shari'a ba. Haka nan ma masu hikima ba za su bar yin shawara ba, haka nan kuma annabi ba zai bar yin magana ba! Ku zo mu kai ƙararsa, kada mu kula da abin da zai faɗa.”


Saboda haka mutane suke tsoronsa, Bai kula da waɗanda suke ɗaukar kansu su masu hikima ba ne.”


Amma wannan ƙanƙanen abu ne a gare ka, ya Allah. Ka kuma yi alkawari, cewa za ka tsawaita kwanakin zuriyar bawanka, ka ɗauke ni kamar ni wani babban mutum ne, ya Ubangiji Allah.


Kada ya kusaci gawa, ko gawar mahaifinsa, ko ta mahaifiyarsa don kada ya ƙazantu.


Musa kuma ya ce wa Haruna, da 'ya'yansa maza, wato, Ele'azara da Itamar, “Kada ku bar gashin kanku barkatai, kada kuma ku kyakketa rigunanku don kada ku mutu, don kada Ubangiji ya yi fushi da taron jama'a duka, amma 'yan'uwanku, wato, dukan Isra'ilawa, suna iya kuka saboda waɗanda Ubangiji ya ƙone.


Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”


Na gama ka da Allah, da Almasihu Yesu, da kuma zaɓaɓɓun mala'iku, ka kiyaye waɗannan abubuwa ƙwarai da gaske, kada ka yi kome da tāra.


sai dai kamar yadda Allah ya yarda da mu, ya damƙa mana amanar bishara, haka muke sanar da ita, ba domin mu faranta wa mutane rai ba, sai dai domin mu faranta wa Allah, shi da yake jarraba zukatanmu.


Kai kaɗai nake so, ya Ubangiji, Na yi alkawari in yi biyayya da dokokinka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ