Gama ka keɓe su daga sauran dukan al'ummai domin su zama jama'arka kamar yadda ka faɗa ta bakin bawanka Musa, sa'ad da ka fito da kakanninmu daga Masar.”
a kuma sa ku ku waye ta idon zuci, domin ku san ko mene ne begen nan da ya kira ku a kai, da kuma ko mene ne yalwar gādonsa mai ɗaukaka a game da tsarkaka,
Sa'an nan Sama'ila ya ɗauki 'yar kwalabar mai, ya zuba wa Saul a kā, ya yi masa sumba, ya ce, “Ubangjiji ne ya keɓe ka, ya naɗa ka sarki a kan jama'arsa.
Tsoro da razana sun aukar musu, Ta wurin ikonka suka tsaya cik kamar dutse, Har jama'arka, ya Ubangiji, suka haye, I, jama'arka, ya Ubangiji, suka haye,
Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama'a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”
Ka tuna da jama'arka waɗanda ka zaɓa su zama naka tuntuni, Ka tuna da jama'arka waɗanda ka fansa, Don su zama kabilarka. Ka tuna da Dutsen Sihiyona, inda zatinka yake!
Gama Ubangiji Allahnmu ne ya fisshe mu da kakanninmu daga ƙasar Masar, a gidan bauta. Shi ne wanda ya aikata manyan alamu a idonmu, ya kuma kiyaye mu a dukan hanyar da muka bi, da cikin dukan al'umman da muka ratsa.
Ka yardar mini in ga wadatar jama'arka, In yi tarayya da jama'arka da farin cikinsu, In yi farin ciki tare da waɗanda suke murna ta fāriya domin su naka ne.
Ubangiji Mai Runduna zai sa musu albarka, ya ce, “Zan sa muku albarka, ke Masar, jama'ata, da suke Assuriya wadda na halitta, da ke kuma Isra'ila zaɓaɓɓiyar jama'ata.”
Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi, Don su more ta su ci amfaninta, Amma da suka shiga, sun ƙazantar mini da ita, Suka sa ƙasar da na gādar musu ta zama abar ƙyama.