Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 32:50 - Littafi Mai Tsarki

50 Za ka rasu a kan dutsen da za ka hau, za a kai ka wurin mutanen da suka riga ka gidan gaskiya, kamar yadda ɗan'uwanka, Haruna, ya rasu a Dutsen Hor, aka kai shi wurin mutanensa waɗanda suka riga shi gidan gaskiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

50 A can kan dutsen da ka hau za ka mutu a kuma tara ka ga mutanenka, kamar yadda ɗan’uwanka Haruna ya mutu a Dutsen Hor aka kuma tara shi ga mutanensa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 32:50
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ibrahim ya ja numfashinsa na ƙarshe ya kuwa rasu cikin kyakkyawan tsufa, tsoho ne mai shekaru masu yawa, aka kai shi ga jama'arsa, waɗanda suka riga shi.


Bisa ga umarnin Ubangiji, Haruna firist ya hau Dutsen Hor inda ya rasu a rana ta fari ga watan biyar a shekara ta arba'in ta fitowar jama'ar Isra'ila daga ƙasar Masar.


“Ka yi tafiyarka ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.”


Sa'ad da Yakubu ya gama yi wa 'ya'yansa maza wasiyya, sai ya hau da ƙafafunsa bisa kan gado, Ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.


Waɗannan su ne shekarun Isma'ilu a duniya, shekara ɗari da talatin da bakwai, ya ja numfashinsa na ƙarshe ya rasu, aka kai shi ga jama'arsa waɗanda suka riga shi.


Kai kuwa, cikin salama za ka koma ga iyayenka, da kyakkyawan tsufa za a binne ka.


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada.


Nan fa, a ƙasar Mowab, Musa bawan Ubangiji, ya rasu kamar yadda Ubangiji ya faɗa.


Ubangiji ya ce wa Musa, “Ga shi, za ka rasu ka tarar da kakanninka. Wannan jama'a kuwa za ta fara kaucewa daga hanya, su bi gumakan ƙasar da za su shiga, su zauna. Za su rabu da ni, su ta da alkawarina wanda na yi da su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ