M.Sh 32:47 - Littafi Mai Tsarki47 Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202047 Ba kalmomi kurum ba ne dominku, amma har ranku ma. Ta wurinsu za ku yi tsawon rai a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.” အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Idan kuka kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku waɗanda nake umartarku da su yau, idan kuma kun ƙaunaci Ubangiji Allahnku, kuna yin tafiya cikin tafarkunsa, kuna kiyaye umarnansa, da dokokinsa, da farillansa, to, za ku rayu, ku riɓaɓɓanya, Ubangiji Allahnku kuwa zai sa muku albarka cikin ƙasar da za ku shiga, ku mallake ta.