45 Sa'ad da Musa ya gama hurta waɗannan kalmomi ga Isra'ila,
45 Sa’ad da Musa ya gama karanta waɗannan kalmomi ga dukan Isra’ila,
Sai Musa da Joshuwa ɗan Nun suka zo, suka hurta dukan kalmomin wannan waƙa a kunnen jama'a.
ya ce musu, “Ku riƙe dukan waɗannan kalmomi a zuciyarku, waɗanda nake yi muku kashedi da su a yau don ku umarci 'ya'yanku su kiyaye dukan maganar dokokin nan sosai.