Idan kun yi rantsuwa kuka ce, ‘Har da ran Ubangiji kuwa,’ Da gaskiya, da aminci, da adalci, Sa'an nan sauran al'umma za su so in sa musu albarka, Za su kuma yabe ni.”
Duk lokaci kuma da rayayyun halittan nan suka ɗaukaka wanda yake zaune a kan kursiyin, yake kuma raye har abada abadin, suka girmama shi, suka kuma gode masa,
sai dattawan nan ashirin da huɗu suka fāɗi a gaban wanda yake a zaune a kan kursiyin, su yi masa sujada, shi da yake a raye har abada abadin, su kuma ajiye kambinsu a gaban kursiyin, suna waƙa, suna cewa,
Domin haka ku ji maganar Ubangiji, dukanku mutanen Yahuza da yake zaune a ƙasar Masar. ‘Ni Ubangiji na rantse da sunana Maɗaukaki, cewa ba zan yarda kuma wani mutumin Yahuza da yake ƙasar Masar ya ambaci sunana da yin rantsuwa, cewa ya rantse da zatin Ubangiji ba.’
Ka ce musu, ni Ubangiji Allah, na ce a ranar da na zaɓi Isra'ila na ta da hannuna, na rantse wa zuriyar Yakubu, na kuma bayyana kaina a gare su a ƙasar Masar, cewa ni ne Ubangiji Allahnsu,
a ran nan na rantse musu, cewa zan fito da su daga ƙasar Masar, zuwa wata ƙasa wadda na samo musu, ƙasar da take da yalwar albarka, wato ƙasa mai albarka duka.
Da yake zan karkashe adalai da mugaye daga cikinta, domin haka takobina zai fito daga cikin kubensa, ya karkashe dukan mutane daga Negeb wajen kudu, har zuwa arewa.
Sai mutumin da yake sāye da rigar lilin ɗin, wanda yake tsaye a gaɓar kogin ya ɗaga hannuwansa sama, sa'an nan ya rantse da wanda yake rayayye har abada, ya ce, “Za a yi shekara uku da rabi. Za a kammala waɗannan abubuwa, sa'ad da aka gama ragargaje ikon tsarkakan mutane.”