Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.
“A kan turaren da ku da kakanninku, da sarakunanku, da shugabanninku, da mutanen ƙasar, kuka ƙona a garuruwan Yahuza da a titunan Urushalima, kuna tsammani Ubangiji bai san su ba, ko kuna tsammani ya manta?