Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”
Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, ‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.’ ”
Duk wanda yake na mutanensa da yake nan Ubangiji Allahnsa ya kasance tare da shi, bari ya haura zuwa can Urushalima ta ƙasar Yahuza don ya sāke gina Haikalin Ubangiji, Allah na Isra'ila, shi ne Allah wanda ake masa sujada a Urushalima.
Ba wata maitar da za ta cuci Yakubu, Ba kuwa sihirin da zai cuci Isra'ilawa. Yanzu za a ce, ‘Duba irin abin da Allah ya yi domin Yakubu, wato Isra'ilawa!’
Sarkinsu zai tsere saboda razana, shugabannin sojojinsu kuwa za su firgita, har su watsar da tutocinsu na yaƙi.” Ubangiji ne ya faɗa, Ubangiji da ake yi wa sujada a Urushalima, wanda kuma wutarsa tana ci a can domin hadayu.