Ubangiji ya ce, “Mutanena wawaye ne, Ba su san ni ba, Yara ne dakikai, Ba su da ganewa. Suna gwanance da aikin mugunta, Amma ba su san yadda za su yi nagarta ba.”
Mutanena sun lalace saboda jahilci. Tun da yake sun ƙi ilimi, Ni ma na ƙi ku da zaman firist ɗina. Tun da yake kun manta da umarnan Allahnka, Ni ma zan manta da 'ya'yanku.
Rassan itatuwa sun bushe sun kakkarye, mata kuwa sun tattara, don su riƙa hura wuta da su. Da yake jama'a ba su gane kome ba, Allah Mahaliccinsu ba zai ji tausayinsu ba, ba zai nuna musu jinƙai ba.
'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.
Don haka zan firgita su ba zato ba tsammani, da dūka a kai a kai. Waɗanda suke da hikima za su zama wawaye, dukan wayon nan nasu kuwa ba zai amfana musu kome ba.”