Gama zan aiko miki da masifu na yunwa domin hallakarwa. Zan aiko miki da su don su hallaka ki. Zan kawo miki yunwa mai tsanani, in sa abincinki ya ƙare.
“Ni Ubangiji Allah na ce, ‘Balle fa sa'ad da na aika wa Urushalima da hukuntaina guda huɗu masu zafi, wato takobi, da yunwa, da mugayen namomin jeji, da annoba, don in kashe mutum duk da dabba!
“Amma idan ba za ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ko kuwa ba ku lura kuka aikata umarnansa da dokokinsa waɗanda nake umartar da su yau ba, to, dukan waɗannan la'ana za su auko muku, su same ku.
domin sun rabu da ni, sun ƙona turare ga gumaka don su tsokane ni in yi fushi da aikin hannuwansu. Saboda haka fushina zai ƙuna a kan wurin nan, ba kuwa zai huce ba.’
Ku kashe tsofaffi, da samari, da 'yan mata, da ƙananan yara, da mata, amma kada ku taɓa wanda yake da shaida. Sai ku fara a Haikalina.” Suka kuwa fara da dattawan da suke a gaban Haikalin.