Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 32:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Gama fushina ya kama wuta, Tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za ta cinye duniya da dukan amfaninta, Za ta kama tussan duwatsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Gama fushina ya kama wuta, tana ci har ƙurewar zurfin lahira. Za tă cinye duniya da girbinta, tă kuma sa wuta a tussan duwatsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 32:22
42 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji ya saki fushinsa, Ya zuba fushinsa mai zafi. Ya kunna wa Sihiyona wuta Wadda ta cinye harsashin gininta.


Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina ya kama kamar wuta, zai yi ta ci har abada.”


“Domin haka ni Ubangiji na ce, Ku jira ni zuwa ranar da zan tashi in yi tuhuma. Gama na ƙudura zan tattara al'umman duniya, da mulkoki, Don in kwarara musu hasalata Da zafin fushina, Gama zafin kishina Zai ƙone dukan duniya.


Duwatsu za su narke a ƙarƙashinsa, Kwaruruka za su tsattsage kamar kakin zuma a gaban wuta, Kamar ruwa yana gangarowa daga tsauni.


Za ku rasa abin da yake hannunku daga cikin gādon da na ba ku. Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama da fushina wuta ta kama wadda za ta yi ta ci har abada.”


Wane irin girma madawwamiyar ƙaunarka take da shi a gare ni! Gama ka cece ni daga zurfin kabari.


Wuta kuma ta fito daga wurin Ubangiji ta cinye mutum ɗari biyu da hamsin ɗin nan da suke miƙa hadaya da turare.


yana ta sāka wa waɗanda suke ƙi sanin Allah, da kuma waɗanda suka ƙi bin bisharar Ubangijinmu Yesu.


Ku macizai! Yaya za ku tsere wa hukuncin Gidan Wuta?


In kuwa idonka yana sa ka laifi, to ƙwaƙule shi ka yar. Zai fiye maka ka shiga rai da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu.”


Kada ku ji tsoron masu kisan mutum, amma ba sa iya kashe kurwarsa. Sai dai ku ji tsoron wannan da yake da ikon hallaka kurwar da jikin duka a Gidan Wuta.


Duwatsu sun gan ka, sun ƙame, Ruwaye masu hauka suka gudu. Zurfi kuma ya ta da muryarsa, Raƙuman ruwansa sun tashi.


ni, Ubangiji Allah, ina yin magana da zafin kishina gāba da sauran al'umma, da dukan Edom, gama da farin ciki da raini suka mallaki ƙasata, suka washe ta.’


Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra'ila, Ya kuma bar yi musu taimako A lokacin da abokan gāba suka zo. Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.


Ya ku mutanen Yahuza da na Urushalima, Ku yi wa kanku kaciya domin Ubangiji, Ku kawar da loɓar zukatanku Don kada fushina ya fito kamar wuta, Ya cinye, ba mai iya kashewa, Saboda mugayen ayyukan da kuka aikata.”


Duwatsu da tuddai za su ragargaje, Amma ƙaunar da nake yi miki ba za ta ƙare ba sam. Zan cika alkawarina na salama har abada.” Haka Ubangiji ya faɗa, shi wanda yake ƙaunarki.


An riga an shirya wurin ƙonawa don Sarkin Assuriya. An tsiba itace cike da wurin. Kamar kibritu, numfashin Ubangiji zai cinna masa wuta.


Saboda haka Allah ya aiko da la'ana ta hallaka duniya. Jama'arta suna karɓar sakayyar abin da suka aikata. 'Yan kalilan ne suka ragu da rai.


Ya Ubangiji, ka kware sararin sama, ka sauko, Ka taɓa duwatsu, don su tuƙaƙo da hayaƙi.


Wuta tana tafe a gabansa, tana cinye maƙiyansa Waɗanda suke kewaye da shi.


Kamar yadda wuta take cin jeji, Kamar yadda harshen wuta yake ƙone tuddai,


Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, Ko da duniya za ta girgiza, Duwatsu kuma su fāɗa cikin zurfafan teku,


Ubangiji zai hallaka su kamar harshen wuta, sa'ad da ya bayyana. Ubangiji zai cinye su a cikin fushinsa, Wuta kuma za ta cinye su ƙurmus.


Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la'anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya.


Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.


Haka fa, su da dukan abin da yake nasu suka gangara zuwa lahira da rai.


Gama a kishina da zafin hasalata na hurta, cewa a wannan rana za a yi babbar girgiza a ƙasar Isra'ila.


A wahayin da Ubangiji ya nuna mini, na gan shi yana shirin hukunta jama'arsa da wuta. Wutar ta ƙone babbar teku, har ma ta fara ƙone ƙasar.


Dukan wuraren zaman Yakubu, Ubangiji ya hallakar ba tausayi, Da fushinsa kuma ya rurrushe kagaran Sihiyona. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulkin.


Ya ja bakansa kamar abokan gāba, Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi. Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa. A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.


Amma aka tumɓuke kurangar inabin da fushi, Aka jefar da ita ƙasa. Iskar gabas ta busar da ita, 'Ya'yanta suka kakkaɓe, Rassanta masu ƙarfi sun bushe, wuta kuwa ta cinye su.


Zan tattaro ku, in hura muku wutar hasalata, za ku narke a cikinta.


Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira. Idan kuwa kun ƙi, Shi zai babbaka jama'ar Yusufu Kamar yadda a kan babbaka da wuta. Wuta za ta ƙone jama'ar Betel, Ba kuwa mai kashe wutar.


Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su A ranar hasalar Ubangiji ba, A cikin zafin kishinsa Dukan duniya za ta hallaka. Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ