Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 32:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Suka sa ni kishi da abin da ba Allah ba, Suka tsokani fushina da gumakansu, Ni kuma zan sa su su yi kishi da waɗanda suke ba mutane ba. Zan tsokane su da wawanyar al'umma.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Sun sa ni kishi ta wurin abin da ba allah ba, suka kuma husata ni da gumakansu na wofi. Zan sa su yi kishi ta wurin waɗanda ba mutane ba; zan sa su yi fushi ta wurin al’ummar da ba ta da sani.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 32:21
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Har wa yau, ina tambaya. Shin, Isra'ila kam, ba su fahimta ba ne? Da farko dai Musa ya ce, “Zan sa ku kishin waɗanda ba al'umma ba ne, Zan kuma sa ku fushi da wata al'ummar marar fahimta.”


Kamar dai yadda ya faɗa a Littafin Yusha'u cewa, “Waɗanda dā ba jama'ata ba, Zan ce da su ‘jama'ata,’ Wadda dā ba abar ƙaunata ba kuma, Zan ce da ita ‘abar ƙaunata.’ ”


Ya bi duk irin hanyoyin Yerobowam ɗan Nebat, da irin zunuban da ya sa jama'ar Isra'ila su yi. Suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu.


Wannan kuwa ya faru saboda zunuban Ba'asha da na ɗansa Ila, da zunuban da suka sa jama'ar Isra'ila su yi, har suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu.


Su waɗanda suke yin sujada ga gumaka marasa amfani Sun daina yi maka biyayya.


Suka sa shi ya yi fushi saboda Masujadansu na arnanci. Suka sa ya ji kishi saboda gumakansu.


Suka sa shi kishi, saboda gumaka, Suka tsokani fushinsa da abubuwan banƙyama.


“Duk da haka yawan mutanen Isra'ila Zai zama kamar yashi a bakin teku, Wanda ba za a iya aunawa ko ƙidayawa ba. Maimakon kuma a ce, ‘Ku ba mutanena ba ne,’ Za a ce, ‘Ku mutanen Allah ne mai rai.’


A cikin gumakan al'ummai akwai mai iya sa a yi ruwa? Sammai kuma su yi yayyafi? Ashe, ba kai ne ba, ya Ubangiji Allahnmu? Domin haka a gare ka muke sa zuciya, Gama kai ne mai yin waɗannan abubuwa duka.”


Kana ƙin waɗanda suke yi wa gumaka sujada, Amma ni na dogara gare ka.


Ashe, har mā tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?


Da fara maganata, Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu, daidai yadda ya sauko mana tun da farko.


Ku ji kukan jama'ata ko'ina a ƙasar, “Ubangiji, ba shi a Sihiyona ne? Sarkinta ba ya a cikinta ne?” Ubangiji ya ce, “Me ya sa suka tsokane ni da sassaƙaƙƙun gumakansu, Da baƙin gumakansu?”


Dukansu dakikai ne wawaye, Koyarwar gumaka ba wani abu ba ne, itace ne kawai!


Kada kuma ku ratse ku bi abubuwa marasa amfani da ba za su amfane ku, ko su cece ku ba, gama ba su da wani amfani.


“Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.


Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba, Ga gumakan da ba su sani ba, Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya, Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.


Mutanen Yahuza suka yi wa Ubangiji zunubi. Suka tsokane shi ya yi fushi saboda zunuban da suka aikata fiye da abin da kakanninsu suka yi.


Suka yi watsi da dokokinsa, da alkawarinsa da ya yi wa kakanninsu, da kuma faɗakarwar da ya yi musu. Suka bi gumakan banza, suka zama banza, suka bi halin al'ummai da suke kewaye da su, waɗanda Ubangiji ya umarce su kada su yi kamarsu.


“Don me zan gafarce ki? 'Ya'yanki sun rabu da ni, Sun yi rantsuwa da gumaka, Na ciyar da su har sun ƙoshi sosai, Suka yi karuwanci, suka ɗunguma zuwa gidajen karuwai,


Yara sukan tara itace, iyaye maza sukan haɗa wuta, iyaye mata sukan kwaɓa ƙullu don su yi wa gunkin nan wadda ake kira sarauniyar sama, waina. Sukan kuma miƙa wa gumaka hadayu na sha domin su tsokane ni.”


Amma ka aikata mugunta fiye da dukan waɗanda suka riga ka, ka yi wa kanka gumaka, da siffofi na zubi, ka tsokane ni in yi fushi, ka yi watsi da ni.


Suka ƙona turare a kan wuraren tsafi na kan tuddai kamar yadda al'ummar da Ubangiji ya kora daga gabansu suka yi. Suka aikata mugayen abubuwa, suka su Ubangiji ya yi fushi.


Ya miƙa ɗansa hadaya ta ƙonawa ya kuma aikata sihiri, ya yi dūba. Ya yi ma'amala da masu mabiya da mayu. Ya aikata mugunta ƙwarai a gaban Ubangiji, ya sa Ubangiji ya yi fushi.


domin sun rabu da ni, sun ƙona turare ga gumaka don su tsokane ni in yi fushi da aikin hannuwansu. Saboda haka fushina zai ƙuna a kan wurin nan, ba kuwa zai huce ba.’


Suka yi ta ƙara sa ni fushi ta wurin rashin kunyarsu. Suka miƙa hadayu irin na arna a ɗakunan tsafi da suke a lambu, suka kuma ƙona turare a kan bagadan arna.


Akwai wata al'umma da ta taɓa sāke gumakanta Ko da yake su ba kome ba ne? Amma mutanena sun sauya darajarsu da abin da ba shi da rai.


Amma mutanena sun manta da ni, Sun ƙona wa gumaka turare. Sun yi tuntuɓe a cikin al'amuransu, a hanyoyin dā, Sun bi ɓarayin hanyoyi, ba su bi karauka ba.


Sai ya miƙa hannu, ya kama zankon kaina. Ruhu kuma ya ɗaga ni bisa tsakanin sama da ƙasa, ya kai ni Urushalima cikin wahayi zuwa ƙofar farfajiya ta ciki, wadda take fuskantar arewa, inda mazaunin siffa ta tsokano kishi yake.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ