Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku, Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura. Ni na halice ku zan kuwa lura da ku, Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”
Kamar yadda ake bi da shanu cikin kwari mai dausayi, haka Ubangiji ya ba mutanensa hutawa. Haka kuma Ubangiji ya bi da mutanensa, ya kuwa kawo ɗaukaka ga sunansa.
Gama Ubangiji Allahnmu ne ya fisshe mu da kakanninmu daga ƙasar Masar, a gidan bauta. Shi ne wanda ya aikata manyan alamu a idonmu, ya kuma kiyaye mu a dukan hanyar da muka bi, da cikin dukan al'umman da muka ratsa.