Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 32:11 - Littafi Mai Tsarki

11 Kamar gaggafar da take kaɗa fikafikanta a kan sheƙarta, Tana rufe da 'yan tsakinta, Ta buɗe fikafikanta, ta kama su, Ta ɗauke su a bisa kafaɗunta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

11 kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta tana rufe ’ya’yanta, ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su tă ɗauke su a kafaɗunta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 32:11
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

‘Kun dai ga abin da na yi da Masarawa, da yadda na ɗauke ku kamar yadda gaggafa take ɗaukar 'yan tsakinta, na kawo ku gare ni.


Ni ne Allahnku, zan kuwa lura da ku, Har lokacin da kuka tsufa kuka yi furfura. Ni na halice ku zan kuwa lura da ku, Zan yi muku taimako in kuwa kuɓutar da ku.”


daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala'ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,


Amma waɗanda suke dogara ga Ubangiji domin taimako Za su ji an sabunta ƙarfinsu. Za su tashi da fikafikai kamar gaggafa, Sa'ad da suke gudu, ba za su ji gajiya ba, Sa'ad da suke tafiya, ba za su ji kasala ba.


Wutsiyarsa ta sharo sulusin taurari, ta zuba su a ƙasa. Sai macijin ya tsaya a gaban matar nan mai naƙuda, don ya lanƙwame ɗan nata in ta haife shi.


Ta wurin bangaskiya muka fahimta, cewa ta faɗar Allah ce aka tsara duniya, har ma abubuwan da ake gani, daga abubuwan da ba a gani ne, suka kasance.


Kamar yadda tsuntsu yake shawagi a kan sheƙarsa don ya kiyaye 'ya'yansa, haka ni, Ubangiji Mai Runduna, zan kiyaye Urushalima in kāre ta kuma.”


Amma aka ba matar fikafikan nan biyu na babban juhurman nan, don ta tashi ta guje wa macijin nan, ta shiga jeji, ta je wurin da za a cishe ta a lokaci ɗaya, da lokatai, da rabin lokaci.


duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen.


A kan Biliyaminu, ya ce, “Shi ƙaunatacce na Ubangiji ne, Yana zaune lafiya kusa da shi, Ubangiji yana yi masa garkuwa dukan yini, Yana zaune a kan kafaɗunsa.”


Ya sauko ta bisa bayan kerubobi, Yana tafe da sauri a kan fikafikan iska.


Gama kamar yadda abin ɗamara yakan kame tam a gindin mutum, haka na sa dukan mutanen Isra'ila da dukan mutanen Yahuza su manne mini domin su zama jama'a, da suna, da yabo, da daraja a gare ni, amma sun ƙi ji.”


Ko da yake ni ne na koya wa Ifraimu tafiya. Na ɗauke su a hannuna, Amma ba su sani ni ne na lura da su ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ