Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya bashe su a hannunku, kuka kuma ci nasara a kansu, sai ku hallaka su sarai. Kada ku yi alkawari da su, kada kuma ku yi musu jinƙai.
Sun yi kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa bawansa, haka kuma Musa ya umarci Joshuwa, haka kuwa Joshuwa ya yi. Ba abin da bai aikata ba cikin dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa.