Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 31:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Gama na sani bayan rasuwata za ku aikata mugunta, ku kauce daga hanyar da na umarce ku. Masifa za ta auko muku a kwanaki masu zuwa saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, za ku tsokani fushinsa da aikin hannuwanku.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Gama na san cewa bayan rasuwata, tabbatacce za ku lalace gaba ɗaya, ku juye daga hanyar da na umarce ku. A kwanaki masu zuwa, masifa za tă auka muku saboda za ku aikata mugunta a gaban Ubangiji, ku tsokane shi har yă yi fushi ta wurin abin da hannuwanku suka yi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 31:29
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma idan mahukuncin ya rasu, sai su sāke kaucewa, su yi zunubi fiye da na kakanninsu. Suna bin gumaka, suna bauta musu, suna kuma yi musu sujada, ba su daina mugayen ayyukansu na rashin aminci da taurin zuciya ba.


Sun aikata mugunta a gabansa, Su ba 'ya'yansa ba ne saboda lalacewarsu, Su muguwar tsara ce, karkatacciya,


Sun yi zurfi cikin rashin gaskiya Kamar a kwanakin Gibeya, Ubangiji zai tuna da muguntarsu. Zai hukunta su saboda zunubansu.


Yakubu ya kirawo 'ya'yansa maza, ya ce, “Ku tattaru wuri ɗaya don in faɗa muku abin da zai same ku a cikin kwanaki masu zuwa:


Da farko dai lalle ne ku fahimci wannan, cewa a can zamanin ƙarshe masu ba'a za su zo suna ba'a, suna biye wa muguwar sha'awarsu,


amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya.


To, Ruhu musamman ya ce, a can wani zamani waɗansu za su fanɗare wa bangaskiya, su mai da hankali ga aljannu masu ruɗi, da kuma koyarwar aljannu,


Har ma a cikinku waɗansu mutane za su taso, suna maganganun da ba sa kan hanya, don su jawo masu bi gare su.


Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”


Bayan kwanaki masu yawa zan ziyarce ka, a cikar waɗannan shekaru, za ka koma ƙasar duwatsun Isra'ila, wadda ta farfaɗo daga masifar yaƙin da ta sha, ƙasa inda jama'a suka tattaru daga sauran al'umma masu yawa, wadda a dā ta yi ta lalacewa, sai da aka fito da mutanenta daga cikin al'ummai, yanzu kuwa dukansu suna zaman lafiya.


An hallaka ki, ke al'umma mai zunubi, ku lalatattun mutane! Zunubinku ya ja ku ƙasa! Kun ƙi Ubangiji, Allah Mai Tsarki na Isra'ila, kun juya masa baya.


Amma na sani akwai wani a Samaniya Wanda a ƙarshe zai zo ya tsaya mini.


‘Ni Ubangiji, na ce zan kawo masifa a kan wannan wuri da a kan mazaunan wurin, wato dukan la'anar da aka rubuta a littafin da aka karanta a gaban Sarkin Yahuza.


Sa'ad da wahala ta same ku, waɗannan abubuwa kuma suka auko muku nan gaba, za ku juyo wurin Ubangiji Allahnku, ku yi masa biyayya.


Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko'ina.


don kada ku yi mugunta, ku sassaƙa wa kanku wata siffar kowane abu, ko siffar mace ko ta namiji,


Sa'an nan Musa ya hurta kalmomin wannan waƙa a kunnen dukan taron jama'ar Isra'ila har ƙarshensu.


Ya ce, ‘Zan ɓoye musu fuskata, Zan ga yadda ƙarshensu zai zama. Gama su muguwar tsara ce, 'Ya'ya ne marasa aminci.


Da suna da hikima, da sun gane wannan, Da za su gane da yadda ƙarshensu zai zama!


Na zo ne don in ganar da kai a kan abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin yana a kan kwanaki na nan gaba ne.”


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Sauka, gama jama'arka da ka fito da su daga ƙasar Masar sun ƙazantar da kansu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ