Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama'ar Isra'ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.”
Kada wannan littafin dokoki ya rabu da bakinka, amma zai zama abin da za ka yi ta tunani a kansa dare da rana domin ka kiyaye, ka kuma aikata bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki, gama ta haka za ka yi albarka cikin hanyarka, ta haka kuma za ka yi nasara.
Ya kuwa rubuta waɗannan kalmomi a littafin Shari'ar Ubangiji. Ya kuma ɗauki wani babban dutse, ya kafa a ƙarƙashin itacen oak a wuri mai tsarki na Ubangiji.
Hilkiya babban firist kuwa ya ce wa Shafan magatakarda, “Na iske littafin dokoki a cikin Haikalin Ubangiji.” Hilkiya kuwa ya ba Shafan littafin, shi kuwa ya karanta shi.