Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 31:19 - Littafi Mai Tsarki

19 “Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra'ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙan nan ta zama shaida a gare ni game da Isra'ilawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 “To, sai ka rubuta wannan waƙa domin kanka, ka koya wa Isra’ilawa, ka kuma sa su rera ta, don tă zama shaida a kansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 31:19
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.


“Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku,


Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe.


Sa'an nan ki tafi wurin sarki, ki ce masa haka.” Sai ya faɗa mata abin da za ta faɗa.


Sa'an nan Musa ya hurta kalmomin wannan waƙa a kunnen dukan taron jama'ar Isra'ila har ƙarshensu.


Za ku koya wa 'ya'yanku su, ku yi ta haddace su, sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.


Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma.


Ko su ji, ko kada su ji, gama su masu tayarwa ne, amma za su sani akwai annabi a cikinsu.


Sa'an nan Ubangiji ya miƙa hannunsa ya taɓa bakina, ya ce mini, “Ga shi, na sa maganata a bakinka.


Ubangiji ya ce, “Amma ni, wannan shi ne alkawarina da su, Ruhuna da yake tare da ku, da kalmomina da na sa a bakunanku, ba za su rabu da bakunanku ba, ko daga bakunan 'ya'yanku, ko na jikokinku, tun daga wannan lokaci har abada.”


Na shimfiɗa sammai, Na kafa harsashin ginin duniya, Na ce wa Sihiyona, ‘Ku jama'ata ne! Na ba ku koyarwata, Na kuwa kiyaye ku da ikona.’ ”


Sai ka yi magana da shi. Ka kuma sa masa maganata a baka, zan kuwa kasance tare da bakinka da bakinsa. Zan kuma sanar da ku abin da za ku yi.


Hakika kuwa, zan ɓoye musu fuskata sabili da muguntar da suka aikata, suka kuma bi gumaka.


Ku rubuta abin da Ubangiji ya aikata don zamani mai zuwa, Don waɗanda ba a haife su ba tukuna, Su ma su yabe shi.


“Ku saurara, ya ku sammai, gama zan yi magana, Bari duniya ta ji maganar bakina.


Sai ya ce wa jama'a, “Wannan dutse shi ne shaida a kanmu, gama ya ji dukan abin da Ubangiji ya faɗa mana, domin haka zai zama shaida a kanku, don kada ku yi wa Allahnku ƙarya.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ