Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 31:13 - Littafi Mai Tsarki

13 domin 'ya'yansu, waɗanda ba su sani ba, su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku dukan kwanakinku cikin ƙasar da za ku haye Urdun, ku mallaka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 ’Ya’yansu, waɗanda ba su san wannan doka ba, dole su ji ta, su kuma koyi tsoron Ubangiji Allahnku muddin ranku a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 31:13
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yau fa ku sani ba da 'ya'yanku nake magana ba, waɗanda ba su sani ba, ba su kuma ga hukuncin Ubangiji Allahnku ba, da girmansa, da ƙarfin ikon dantsensa,


Sai ku koya wa 'ya'yanku su da himma. Za ku haddace su sa'ad da kuke zaune a gida, da sa'ad da kuke tafiya, da sa'ad da kuke kwance, da sa'ad da kuka tashi.


Ku ubanni, kada ku sa 'ya'yanku su yi fushi, sai dai ku goye su da tarbiyya, da kuma gargaɗi ta hanyar Ubangiji.


Ka koya wa yaro yadda zai yi zamansa, zai kuwa tuna da ita dukan kwanakinsa.


Don zuriyarsu ta sani Ubangiji ya sa Isra'ilawa su zauna cikin bukkoki, sa'ad da ya fito da su daga ƙasar Masar. Shi ne Ubangiji Allahnsu.


da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.’


Ku tara dukan jama'a wuri ɗaya, mata da maza, da yara, da baƙin da suke zaune tare da ku a garuruwanku domin su ji, su koyi tsoron Ubangiji Allahnku, su kuma lura su aikata dukan dokokin nan,


Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Lokacin rasuwarka ya yi, sai ka kira Joshuwa, ku shigo alfarwa ta sujada, don in ba shi ragamar mulki.” Sai Musa da Joshuwa suka tafi, suka shiga alfarwa ta sujada.


Zarubabel ɗan Sheyaltiyel kuwa, da Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukan sauran mutane, suka yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnsu, suka kuma yi biyayya da maganar annabi Haggai, kamar yadda Ubangiji Allahnsu ya faɗa masa. Mutane kuwa suka yi tsoron Ubangiji.


Wannan ba magana kurum ba ce, amma ranku ne. Ta wurin wannan magana ce za ku yi tsawon rai a ƙasar da za ku haye Urdun zuwa ciki don ku mallake ta.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ