Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi biyayya da maganarsa, ku manne masa, gama wannan shi ne ranku da tsawon kwanakinku, don ku zauna a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya rantse zai ba kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.”
Waɗannan su ne zantuttukan da Musa ya faɗa wa dukan Isra'ilawa a hayin Urdun cikin jejin Araba daura da Suf, tsakanin Faran, da Tofel, da Laban, da Hazerot, da Dizahab.