Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 30:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ubangiji Allahnku kuwa zai ɗora wa magabtanku da maƙiyanku waɗanda suka tsananta muku waɗannan la'ana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Ubangiji Allahnku zai sa dukan waɗannan la’anoni a kan abokan gābanku waɗanda suke ƙinku, suke kuma tsananta muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 30:7
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ubangiji zai kiyaye ku daga dukan cuce-cuce. Ba zai wahalshe ku da mugayen cuce-cuce na Masar ba, waɗanda kuka sani, amma zai wahalar da duk maƙiyanku da waɗannan mugayen cuce-cuce.


Ubangiji ya ce, “Sa'ad da na gama abin da nake yi a kan Dutsen Sihiyona da cikin Urushalima, zan hukunta Sarkin Assuriya saboda dukan kurarinsa da girmankansa.”


Bal'amu ya ce wa Balak, “Yanzu fa, zan koma wurin mutanena. Ka zo in sanar maka da abinda mutanen nan za su yi wa mutanenka nan gaba.”


A ran nan zan sa Urushalima ta zama dutse mai nauyi ga dukan al'ummai. Duk wanda ya ɗaga ta zai ji wa kansa mugun rauni. Dukan al'umman duniya za su taru su kewaye ta.


“Saboda kama-karyar da ka yi wa Yakubu ɗan'uwanka, Za a sa ka ka sha kunya, Za a hallaka ka har abada.


Ubangiji ya ce, “Mutanen Ammon sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don haɗamarsu ta ƙasa, Suka tsaga mata masu ciki a Gileyad.


Ubangiji ya ce, “Mutanen Edom sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun farauci 'yan'uwansu, Isra'ilawa, Suka ƙi su nuna musu jinƙai. Ba su yarda su huce daga fushinsu ba.


Ubangiji ya ce, “Mutanen Taya sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun kwashe mutanen sun kai ƙasar Edom. Suka karya yarjejeniyar abuta wadda suka yi.


Ubangiji ya ce, “Mutanen Gaza sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun kwashe al'umma duka, sun sayar wa mutanen Edom.


Ubangiji ya ce, “Mutanen Dimashƙu sun ci gaba da yin zunubi. Hakika, zan hukunta su, Don sun zalunci mutanen Gileyad da zalunci mai tsanani.


Ubangiji Allah ya ce, “Tun da yake Filistiyawa sun yi sakayya, sun ɗauki fansa da muguwar zuciya da ƙiyayya marar ƙarewa, don su hallakar,


Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Edom ta ɗaukar wa kanta fansa a kan mutanen Yahuza, ta yi babban laifi da ta ɗaukar wa kanta fansa,


Ubangiji Allah ya ce, “Da yake Mowab da Seyir sun ce mutanen Yahuza sun zama kamar al'ummai,


Gama Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun tafa hannuwanku, kun buga ƙafafunku, kuka yi murna don nuna dukan ƙiyayyarku da ƙasar Isra'ila,


Ka faɗa musu su ji maganar Ubangiji Allah.” Ubangiji Allah ya ce, “Da yake kun ce, ‘Madalla,’ a lokacin da aka ƙazantar da Haikalina, da lokacin da ƙasar Isra'ila ta zama kufai, da lokacin da aka kai mutanen Yahuza bautar talala,


Gama ga shi, na fara sa masifa ta yi aiki cikin birnin da ake kira da sunana. To, kuna tsammani ba za a hukunta ku ba? Sai an hukunta ku, gama ina kawo wa dukan mazaunan duniya takobi. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’


Idan kun kasa kunne a hankali ga maganarsa, kuka aikata dukan abin da na faɗa, sai in zama maƙiyin maƙiyanku da magabcin magabtanku.


Sa'an nan za ku yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, ku kiyaye dukan umarnan nan waɗanda na umarce ku da su yau.


Al'ummar tana kama da ƙaƙƙarfan zaki Sa'ad da yake barci, ba wanda zai yi ƙarfin hali ya tashe shi. Duk wanda ya sa muku albarka zai sami albarka, Duk wanda ya sa muku la'ana zai sami la'ana.”


Domin haka dukan waɗanda suka cinye ku, za a cinye su, Dukan maƙiyanku, kowane ɗayansu zai tafi bauta, Waɗanda suka washe ku, za a washe su. Dukan waɗanda suka kwashe ku ganima, su ma za a kwashe su ganima.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ