Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 30:3 - Littafi Mai Tsarki

3 sa'an nan Ubangiji Allahnku zai komo da ku daga bauta, ya yi muku jinƙai. Zai tattaro ku daga cikin al'ummai inda ya warwatsa ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 a sa’an nan ne Ubangiji Allahnku zai yi muku jinƙai, yă ji tausayinku, yă kuma sāke tattara ku daga dukan al’ummai inda ya warwatsa ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 30:3
33 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Za ku same ni, ni Ubangiji na faɗa, zan mayar muku da arzikinku, in tattaro ku daga cikin dukan al'ummai da dukan wurare inda na kora ku, ni Ubangiji na faɗa, zan komo da ku a wurin da na sa a kwashe ku a kai ku zaman talala.’ ”


Zan kwaso ku daga cikin al'ummai, in tattaro ku daga dukan ƙasashe, in kawo ku cikin ƙasarku.


Ko da ya sa ɓacin rai, Zai ji tausayi kuma, Saboda tabbatacciyar ƙaunarsa mai yawa.


Ubangiji yana rayar da Urushalima, Yana komo da waɗanda aka kai su baƙunci a wata ƙasa.


haka su ma da suke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu jinƙai kamar yadda aka yi muku.


Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa, Haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.


Ko su ma, in dai ba su nace wa rashin bangaskiyarsu ba, sai a ɗaura aure da su, domin Allah yana da ikon sāke mai da su.


“Ku ji maganar Ubangiji, Ya ku al'ummai, Ku yi shelarsa har a ƙasashen da suke nesa, na gāɓar teku. Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsa Isra'ila zai tattaro ta, Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayi yakan kiyaye garkensa.’


Haka Ubangiji Allah, shi wanda ya tattara Isra'ilawa korarru, ya faɗa, ya ce, “Zan ƙara tattaro waɗansu, bayan waɗanda na riga na tattara.”


Ta haka nan ne Isra'ila duka za su sami ceto, kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mai Ceto zai zo daga Sihiyona, Zai kuma kawar da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu,”


Ga shi, ina tare da kai, zan kiyaye ka duk inda ka tafi, zan kuwa komo da kai ƙasan nan, gama ba zan rabu da kai ba, sai na aikata abin nan da na hurta maka.”


Isra'ila ya ce wa Yusufu, “Ga shi, ina bakin mutuwa, amma Allah zai kasance tare da kai, zai kuma sāke komar da kai ƙasar kakanninka.


Ubangiji zai warwatsa ku cikin al'ummai. Za ku ragu kaɗan daga cikin al'ummai inda Ubangiji ya warwatsa ku.


Kada ku ɗauka daga cikin abin da aka haramta don zafin fushin Ubangiji ya huce, ya yi muku jinƙai, ya ji tausayinku, ya kuma riɓaɓɓanya ku ma kamar yadda ya rantse wa kakanninku,


Amma idan kun juyo wurina, kun kiyaye umarnaina, kun aikata su, ko da yake an warsatsar da ku can nesa, zan tattaro ku, in kawo ku wurin da na zaɓa domin in sa sunana ya kahu a wurin.’


Ubangiji kuwa ya mayar wa Ayuba da dukiyarsa, sa'ad da ya yi addu'a domin abokansa, sai Ubangiji ya mayar masa da riɓin abin da yake da shi dā.


Ya komo da ku daga ƙasashen waje, Daga gabas da yamma, kudu da arewa.


A wannan rana Ubangiji kansa zai hukunta jama'arsa, Isra'ila, daga wannan iyakar ƙasa zuwa waccan, tun daga Yufiretis har zuwa iyakar Masar. Zai raba tsakanin nagari da mugu.


Ga abin da Ubangiji ya faɗa a kan mugayen maƙwabtan Isra'ila waɗanda suka taɓa gādon da ya ba jama'arsa Isra'ila su gada. “Saboda haka zan tumɓuke su daga cikin ƙasarsu. Zan kuma tumɓuke mutanen Yahuza daga cikinsu.


Ku ce masa, “Ka cece mu, ya Allah Mai Cetonmu, Ka tattara mu, ka kuɓutar da mu daga al'ummai, Domin mu gode maka, Mu kuma yabi sunanka mai tsarki.”


Kada ku ji tsoro, ina tare da ku! “Daga gabas mafi nisa, da kuma yamma mafi nisa, Zan kawo jama'arku zuwa gida.


“A ɗan ƙanƙanen lokaci na rabu da ke, Amma da ƙauna mai zurfi zan sāke karɓarki.


Sa'an nan zan tattaro sauran garkena daga wuraren da aka warwatsa su, zan komo da su cikin garkensu, zan sa su hayayyafa su riɓaɓɓanya.


“Saboda haka ka ce, ‘Ni Ubangiji na ce, zan tattaro ku daga cikin al'ummai, da ƙasashen da aka warwatsa ku, ni kuwa zan ba ku ƙasar Isra'ila.’


Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allahnsu, domin na kore su daga ƙasarsu zuwa bautar talala cikin al'ummai, sa'an nan na sāke tattaro su zuwa cikin ƙasarsu. Daga cikinsu ba zan bar ko ɗaya a cikin al'ummai ba.


Zai sāke jin juyayinmu, Ya tattake muguntarmu a ƙarƙashin ƙafafunsa. Za ka jefar da zunubanmu a cikin zurfin teku.


Ko da yake na watsar da su cikin al'ummai, Duk da haka za su riƙa tunawa da ni daga ƙasashe masu nisa. Su da 'ya'yansu za su rayu, su komo.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ