Ina kiran sama da duniya su zama shaidu a kanku yau, cewa na sa rai da mutuwa a gabanku, da albarka da la'ana. Ku zaɓi rai fa, don ku rayu, ku da zuriyarku.
“Saboda ƙaunar da Allah ya yi wa duniya har ya ba da makaɗaicin Ɗansa, domin duk wanda ya gaskata da shi kada ya hallaka, sai dai ya sami rai madawwami.
“Sa'ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la'ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al'ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku,
Ya kai mutum, ya riga ya nuna maka abin da yake mai kyau. Abin da Ubangiji yake so gare ka, shi ne Ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata alheri, Ka bi Allah da tawali'u.