29 “Sai muka zauna a kwari daura da Bet-feyor.”
29 Sai muka zauna a kwari kusa da Bet-Feyor.
Aka binne shi cikin kwarin ƙasar Mowab, kusa da Betfeyor, amma ba wanda ya san inda aka binne shi har yau.
a hayin Urdun a kwari daura da Bet-feyor, a ƙasar Sihon, Sarkin Amoriyawa, mazaunan Heshbon, waɗanda Musa da Isra'ilawa suka ci da yaƙi sa'ad da suka fita daga ƙasar Masar.
Ta haka Isra'ilawa suka shiga bautar gumakan Ba'al na Feyor. Sai Ubangiji ya husata da Isra'ilawa.
Idanunku sun ga abin da Ubangiji ya yi a Ba'al-feyor, yadda Ubangiji Allahnku ya hallaka dukan mutane daga cikinku da suka bauta wa Ba'al-feyor.
Sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango a Shittim, maza suka fara yin lalata da matan Mowabawa.
da Bet-feyor, da gangaren Fisga, da Betyeshimot.