Ba ku za ku yi wannan yaƙi ba, ku dai, ku jā dāga, ku tsaya kurum ku ga nasarar da Ubangiji zai ciwo muku, ya Yahuza da Urushalima. Kada ku ji tsoro ko ku razana, gobe ku fita ku tsaya gāba da su, gama Ubangiji yana tare da ku.’ ”
Ba da takubansu suka ci ƙasar ba, Ba kuwa da ikonsu suka rinjayi ƙasar ba, Amma da ikonka ne da kuma ƙarfinka, Ta wurin tabbatar musu kana tare da su, Kana nuna musu kana ƙaunarsu.
Ga shi kuwa, Allah yana tare da mu, shi ne shugabanmu, firistocinsa kuwa suna da ƙahon da akan busa lokacin yaƙi, don su busa kira na yin yaƙi. Ya ku Isra'ilawa, kada ku yi yaƙi da Ubangiji, Allah na kakanninku, gama ba za ku yi nasara ba.”
Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Kada ka ji tsoronsa, gama na bashe shi a hannunka duk da jama'arsa, da ƙasarsa. Za ka yi masa yadda ka yi wa Sihon, Sarkin Amoriyawa wanda ya zauna a Heshbon.”
“A lokacin kuwa na umarci Joshuwa na ce, ‘Ai, da idonka ka ga dukan abin da Ubangiji Allahnku ya yi wa waɗannan sarakuna biyu. Haka nan kuwa Ubangiji zai yi wa mulkoki waɗanda za ku haye zuwa wurinsu.
“Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, idan kun ga dawakai, da karusai, da sojoji da yawa fiye da naku, kada ku ji tsoronsu. Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar yana tare da ku.
Kafafun karusansu suka fara kwaɓewa, da ƙyar ake jansu. Daga nan Masarawa suka ce, “Mu guje wa Isra'ilawa, gama Ubangiji yana yaƙi dominsu gāba da Masarawa.”