Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 29:27 - Littafi Mai Tsarki

27 Saboda haka Ubangiji ya husata da wannan ƙasa, ya kawo mata kowace irin la'anar da aka rubuta a wannan littafin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

27 Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan wannan ƙasa, har ya kawo dukan la’anoni da aka rubuta a wannan littafi a kanta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 29:27
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka tafi suka bauta wa gumaka, suka yi musu sujada, gumakan da ba su san su ba, ba Ubangiji ne ya ba su ba.


A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.


‘Ga shi, zan aukar da masifa a wurin nan, da a mazaunan wurin, bisa ga dukan maganar littafin nan wanda Sarkin Yahuza ya karanta,


Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai da mutanen Urushalima da dukan mutanen Yahuza, sai ya kore su daga gabansa. Zadakiya kuwa ya tayar wa Sarkin Babila.


“Sa'ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la'ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al'ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku,


Ubangiji zai hukunta Isra'ila kamar yadda akan girgiza iwa a baƙin rafi, zai tumɓuke Isra'ila daga wannan ƙasa mai albarka wadda ya ba kakanninsu, ya kuma watsar da su a hayin Kogin Yufiretis, domin sun yi wa kansu gumaka don sun tsokani Ubangiji ya yi fushi.


Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can. Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.


Za ka yi fushi da mu har abada? Ba za ka taɓa hucewa ba?


“Sa'ad da mutanenki suka ce, ‘Me ya sa Ubangiji Allahnmu ya yi mana waɗannan abubuwa duka?’ Sai ki ce musu, ‘Kamar yadda kuka rabu da ni kuka bauta wa gumaka a ƙasarku, haka kuma za ku bauta wa baƙi a ƙasar da ba taku ba.’ ”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ