Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 29:10 - Littafi Mai Tsarki

10 “Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra'ila,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabanninku da manyan mutanenku, dattawanku da hafsoshinku, da kuma dukan sauran mutanen Isra’ila,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 29:10
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai na ga matattu manya da yara, a tsaitsaye a gaban kursiyin, aka kuma buɗe littattafai. Sai kuma aka buɗe wani littafi, wanda yake shi ne Littafin Rai. Aka kuwa yi wa matattu shari'a bisa ga abin da yake a rubuce a cikin littattafan, gwargwadon aikin da suka yi.


Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma'arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwanni, da kuma a cikin duwatsu,


Jama'ar Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron ƙofofi, da mawaƙa, da ma'aikatan Haikali, da dukan waɗanda suka ware kansu daga sauran al'umman waɗansu ƙasashe, domin su bi dokokin Allah, su da matansu, da 'ya'yansu mata da maza, da dai duk waɗanda suke da sani da fahimta,


“Saboda wannan duka muke yin alkawari mai ƙarfi a rubuce. Shugabanninmu kuwa, da Lawiyawanmu, da firistocinmu, suka buga hatimi, suka sa hannu.”


A ran ɗaya ga watan bakwai, sai Ezra, firist, ya kawo Attaura a gaban taron jama'a, mata da maza, da dukan waɗanda za su ji, su fahimta.


Sai Yehoyada da dukan jama'a, da sarkin, suka ɗauki alkawari za su zama jama'ar Ubangiji.


da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.’


Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.


da 'ya'yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa.


Babu wata kalmar da Musa ya umarta, da Joshuwa bai karanta a gaban dukan taron Isra'ilawa ba, tare da mata da ƙanana, da baƙin da suke zaune tare da su.


Suka ƙara da cewa, “A bar su da rai domin su zama masu sarar mana itace, da masu ɗebo mana ruwa.”


Ubangiji kuma ya yi ta bayyana a Shilo inda ya bayyana kansa ga Sama'ila, ya kuma yi magana da shi. Duk lokacin da Sama'ila ya yi magana dukan mutanen Isra'ila suna kasa kunne.


A wannan lokaci Isra'ilawa suka yi shiri su yi yaƙi da Filistiyawa, Isra'ilawa suka kafa sansaninsu a Ebenezer, Filistiyawa kuma suka kafa nasu a Afek.


A sa'an nan kuwa mutanen Yahuza suna tsaye a gaban Ubangiji, su da ƙananansu, da matansu, da 'ya'yansu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ