Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 28:64 - Littafi Mai Tsarki

64 “Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

64 Sa’an nan Ubangiji zai watsar da ku cikin dukan al’ummai, daga wannan bangon duniya zuwa wancan. A can za ku bauta waɗansu alloli, allolin itace da na dutse, waɗanda ko ku, ko kakanninku, ba ku sani ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 28:64
27 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan sa a kawo muku yaƙi a warwatsa ku a baƙin ƙasashe, ƙasarku za ta zama kufai, biranenku kuwa za su lalace.


Don haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku ba ku sani ba. A can za ku bauta wa gumaka dare da rana, gama ba zan nuna muku ƙauna ba.’


Ka tuna da maganar da ka umarci bawanka Musa cewa, ‘Idan kun yi rashin aminci, zan warwatsa ku cikin al'ummai.


“Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu.


Za a kashe waɗansu da kaifin takobi, a kuma kakkama waɗansu a kai su bauta zuwa ƙasashen al'ummai duka. Al'ummai kuma za su tattake Urushalima, har ya zuwa cikar zamaninsu.”


“Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu.


Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”


“Ku tambaya mana, ko a kwanakin dā kafin zamaninku, tun ma daga lokacin da Allah ya yi mutum a duniya, ku tantambaya daga wannan kusurwa ta samaniya zuwa waccan, ko wani babban abu irin wannan ya taɓa faruwa, ko kuma an taɓa jin labarin irinsa?


Suka tafi suka bauta wa gumaka, suka yi musu sujada, gumakan da ba su san su ba, ba Ubangiji ne ya ba su ba.


“Sa'ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la'ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al'ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku,


Suka miƙa hadayu ga aljannun da ba Allah ba, Ga gumakan da ba su sani ba, Sababbin allolin da aka shigo da su daga baya, Waɗanda kakanninku ba su ji tsoronsu ba.


Na ce, zan watsar da su, in sa a manta da su cikin mutane.


A shekara ta tara ta sarautar Hosheya, Sarkin Assuriya ya ci Samariya, ya kwashe Isra'ilawa zuwa Assuriya, ya ajiye su a Hala, da Habor a bakin kogin Gozan, da cikin garuruwan Mediyawa.


Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can. Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.


Ka bari aka yanyanka mu kamar tumaki, Ka warwatsar da mu a baƙuwar ƙasa.


Zan sa jama'a su tafi nesa, in sa ƙasar duka ta zama kango.


Zan watsa su cikin sauran al'umma waɗanda su da kakanninsu ba su san su ba, zan sa takobi ya bi su don in hallaka su.


Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina ya kama kamar wuta, zai yi ta ci har abada.”


Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba, Da bauta mai tsanani. Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma, Amma ba ta sami hutawa ba, Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.


Na rantse musu a jeji, cewa zan warwatsar da su cikin sauran al'umma, da sauran ƙasashe


Na warwatsa su cikin al'ummai, suka kuwa warwatsu cikin ƙasashe. Na hukunta su gwargwadon halinsu da ayyukansu.


Na sa guguwa ta warwatsa su a cikin al'ummai da ba su san su ba. Ƙasar da suka bari ta zama kango, ba mai kai da kawowa a cikinta. Ƙasa mai kyau ta zama kango.”


kada ku yarda, kada ku saurare shi. Kada kuma ku ji tausayinsa, kada ku haƙura da shi ko ku ɓoye shi.


“Zan umarta a rairayi jama'ar Isra'ila Da matankaɗi kamar hatsi. Zan rairaye su daga cikin sauran al'umma, Duk da haka ko ƙwaya ɗaya ba za ta salwanta ba.


“Ki raira waƙa, ki yi farin ciki, ya Sihiyona, gama ina zuwa, in zauna a tsakiyarki! Ni Ubangiji na faɗa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ