6 “Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita.
6 Za ku zama masu albarka sa’ad da kuka shiga, za ku kuma zama masu albarka sa’ad da kuka fita.
Zai kiyaye shigarka da fitarka, Tun daga yanzu har abada.
Yanzu sai ka ba ni hikima da sani yadda zan iya kai da kawowa a gaban wannan jama'a, gama wa zai iya mulkin wannan jama'a taka mai yawa haka?”
mutumin da zai shugabance su cikin yaƙi, don kada taron jama'ar Ubangiji su zama kamar tumakin da ba su da makiyaya.”
Ka sani Abner ɗan Ner ya zo ya ruɗe ka ne, ya san fitarka da shigarka, ya kuma san dukan abin da kake yi.”
Ya ce, “Yau shekarata ɗari da ashirin ne, ba na iya kaiwa da komowa. Ubangiji kuwa ya ce mini, ‘Ba za ka haye wannan Urdun ba.’
“Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.
“Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.
“Da la'ana za ku shiga, da la'ana kuma za ku fita.
Allah kuwa ya ce wa Bal'amu, “Ba za ka tafi tare da su ba, ba kuwa za ka la'anta su ba, gama albarkatattu ne su.”