M.Sh 28:58 - Littafi Mai Tsarki58 “Idan ba ku lura, ku aikata dukan maganar dokokin nan da aka rubuta a wannan littafi ba, domin ku ji tsoron sunan nan mai ɗaukaka, mai kwarjini, wato sunan Ubangiji Allahnku, အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202058 In ba ku lura kuka bi dukan kalmomi wannan doka, waɗanda an rubuta a wannan littafi ba, ba ku kuma girmama wannan suna mai ɗaukaka da kuma mai banrazana na Ubangiji Allahnku ba, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Waɗannan Lawiyawa kuma, wato Yeshuwa, da Kadmiyel, da Bani, da Hashabnaiya, da Sherebiya, da Hodiya, da Shebaniya, da Fetahiya su ne suka yi kiran sujada, suka ce, “Ku miƙe tsaye, ku yabi Ubangiji Allahnku, Ku yabe shi har abada abadin. Bari kowa ya yabi maɗaukakin sunanka, ya Ubangijii, Ko da yake ba yabon da ɗan adam zai yi har ya isa.”