Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 28:55 - Littafi Mai Tsarki

55 domin kada ya ba wani daga cikinsu naman 'ya'yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

55 ba kuwa zai ba waninsu wani naman ’ya’yansa da yake ci ba. Gama dukan abin da ya rage masa ke nan saboda wahalar da abokan gābanku za su gasa muku a lokacin da ake kwanton wa dukan biranenku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 28:55
7 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A kan rana ta tara a watan huɗu na wannan shekara, yunwa ta tsananta ƙwarai a birnin. Mutane suka rasa abin da za su ci.


Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce wa Irmiya ya tafi, ya faɗa wa Zadakiya Sarkin Yahuza cewa, “Ni Ubangiji, zan ba da wannan birni a hannun Sarkin Babila, zai kuwa ƙone shi da wuta.


Ku haura, ku lalatar da gonar kurangar inabinta, Amma kada ku yi mata ƙarƙaf, Ku sassare rassanta, Gama su ba na Ubangiji ba ne.


Za ku ci naman 'ya'yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi.


Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan'uwansa, da matarsa, da 'ya'yansa da suka ragu,


Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da 'yarta.


Zan sa su ci naman 'ya'yansu mata da maza. Kowa zai ci naman maƙwabcinsa cikin damuwa a lokacin da za a kewaye su da yaƙi, zai sha wahala daga wurin abokan gābansa da waɗanda suke neman ransa.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ