Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 28:52 - Littafi Mai Tsarki

52 Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

52 Za su kuwa kewaye ku a dukan garuruwanku, har sai katangarku masu tsayi wadda kuke dogara gare su, sun fāɗi ko’ina a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 28:52
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sarki ya yi fushi, ya tura sojansa, suka hallaka masu kisankan nan, suka ƙone garinsu ƙurmus.


Gama zan tattara dukan al'ummai su yi yaƙi da Urushalima. Za a ci birnin, a washe gidajen. Za a yi wa mata faɗe. Za a kai rabin mutanen birnin bauta, amma za a bar sauran mutanen a cikin birnin.


“Ga shi, ina gab da sa Urushalima ta zama ƙoƙon sa tangaɗi ga dukan al'ummai da yake kewaye. Yaƙin da zai kewaye Urushalima zai shafi Yahuza ita ma.


Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara.


Kaldiyawa kuwa za su komo su yi yaƙi da wannan birni. Za su ci birnin, su ƙone shi da wuta.


Gama haka Ubangiji ya ce, “Ga shi, ina jefar da mazaunan ƙasar daga ƙasarsu a wannan lokaci, Zan kawo musu wahala, za su kuwa ji jiki.”


Ubangiji ya yi alkawari mai ƙarfi, Ta wurin ikonsa kuwa zai cika shi. “Hatsinku ba zai ƙara zama abincin abokan gābanku ba, Baƙi ba za su ƙara shanye ruwan inabinku ba.


An lalatar da ƙasarku, an ƙone biranenku ƙurmus. Kuna gani, baƙi suka ƙwace ƙasarku, suka mai da ko'ina kufai.


A shekara ta goma sha huɗu ta sarautar sarki Hezekiya, sai Sennakerib, Sarkin Assuriya, ya kawo wa dukan birane masu garu na Yahuza yaƙi, ya kuwa ci su.


Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku.


Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko 'ya'yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku.


Sai muka dafa ɗana muka cinye. Kashegari kuwa na ce mata ta kawo ɗanta mu ci, amma sai ta ɓoye shi.”


Ku tattara kayayyakinku, Ku mazaunan wurin da aka kewaye da yaƙi.


Dukan wuraren zaman Yakubu, Ubangiji ya hallakar ba tausayi, Da fushinsa kuma ya rurrushe kagaran Sihiyona. Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulkin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ