Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 28:49 - Littafi Mai Tsarki

49 Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

49 Ubangiji zai kawo al’umma daga nesa, daga iyakar duniya, ta sauko a kanku kamar gaggafa, al’ummar da ba ku san yarenta ba,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 28:49
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Masu runtumarmu sun fi gaggafar da take tashi sama sauri. Sun fafare mu a kan duwatsu, Suna fakonmu a cikin jeji.


Wani zai tashi da sauri, ya yi sama kamar gaggafa. Zai buɗe fikafikansa a kan Bozara. Zukatan sojojin Edom za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.”


“Ni Ubangiji na ce, Wani zai yi firiya da sauri kamar gaggafa, Zai shimfiɗa fikafikansa a kan Mowab.


Ubangiji ya ce, “Ki sa ƙaho a bakinki, Kamar gaggafa, haka maƙiyi ya kawo sura a kan ƙasar Ubangiji, Domin mutanena sun ta da alkawarina, Sun kuma keta dokokina.


Ka ce, Ubangiji Allah ya ce, ‘Wata babbar gaggafa mai manyan fikafikai, da dogayen gasusuwan fikafikai da gasusuwa da yawa masu launi iri iri, ta zo Lebanon ta ciri kan itacen al'ul.


“Ka tambayi mutanen Isra'ila, 'yan tawayen nan cewa, ‘Ba ku san ma'anar waɗannan abubuwa ba?’ Ka faɗa musu, cewa Sarkin Babila ya zo Urushalima, ya tafi da sarkinta da shugabanninta zuwa Babila.


A rubuce yake a cikin littattafai masu tsarki cewa, “Zan yi magana da jama'an nan ta wurin mutane masu baƙin harsuna, da kuma ta harshen baƙi, duk da haka kuwa ba za su saurare ni ba, in ji Ubangiji.”


Inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.


Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara.


Duba, ga abokin gāba yana zuwa kamar gizagizai, Karusan yaƙinsa suna kama da guguwa, Dawakansa sun fi gaggafa sauri. Kaitonmu, mun shiga uku!


Jiragen ruwa kuwa za su zo daga Kittim, Za su wahalar da Assuriya da Eber, Su kuma da kansu za su lalace.”


ba wurin waɗansu mutane dabam waɗanda suke da baƙon harshe mai wuya ba, wato harshen da ba ka sani ba. Da na aike ka wurin irin mutanen nan da za su ji.


Zo mu sauka, mu dagula harshensu, domin kada su fahimci maganar juna.”


Ya ba da wannan umarni ga jama'ar Isra'ila, A lokacin da ya fita gāba da ƙasar Masar. Na ji wata murya da ban saba ji ba tana cewa,


“A lokacin nan, Ubangiji zai yi feɗuwa ya kirawo Masarawa su zo kamar ƙudaje daga manisantan mazaunan Kogin Nilu, ya kuma kirawo Assuriyawa su zo daga ƙasarsu kamar ƙudajen zuma.


Ba za ku ƙara ganin baƙin nan masu girmankai, masu magana da harshen da ba ku fahimta ba!


Sa'an nan annabi Ishaya ya je wurin sarki Hezekiya, ya tambaye shi ya ce, “Daga ina waɗannan mutane suka zo? Me kuma suka faɗa maka?” Hezekiya ya amsa ya ce, “Daga ƙasa mai nisa suka zo, wato daga ƙasar Babila.”


‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku.


Kamannin dabba ta fari irin ta zaki ce, amma tana da fikafikan gaggafa. Ina kallo, sai aka fige fikafikanta, aka ɗaga ta sama, aka sa ta tsaya a kan ƙafafu biyu kamar mutum, aka ba ta tunani irin na mutum.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ