“Idan akwai yunwa a ƙasar, ko kuma akwai annoba, ko burtuntuna, ko fumfuna, ko fāri, ko tsutsa, sun cinye amfanin gona, idan kuma abokan gāba sun kawo wa jama'arka yaƙi har ƙofar birninsu, duk dai irin annoba da ciwon da yake cikinsu,
“Na sa darɓa, da domana Su lalatar da amfanin gonakinku. Fāra kuma ta cinye lambunanku Da gonakin inabinku, da itatuwan ɓaurenku, Da na zaitun ɗinku. Duk da haka ba ku komo wurina ba.