Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 28:36 - Littafi Mai Tsarki

36 “Ubangiji zai bashe ku, ku da sarkin da kuka naɗa wa kanku ga wata al'ummar da ku da kakanninku ba ku sani ba. Can za ku bauta wa gumakan itace da na duwatsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

36 Ubangiji zai kore ku, ku da sarkin da kuka naɗa a bisanku zuwa al’ummar da ku, ko kakanninku ba su sani ba. A can za ku yi wa waɗansu alloli sujada, allolin itace da na dutse.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 28:36
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don haka zan fitar da ku daga wannan ƙasa zuwa wata ƙasa wadda ku ko kakanninku ba ku sani ba. A can za ku bauta wa gumaka dare da rana, gama ba zan nuna muku ƙauna ba.’


Sai Nebuzaradan shugaban sojojin, ya kwashe sauran mutanen da suka ragu a birnin, da waɗanda suka gudu zuwa wurin Sarkin Babila, da sauran da suka ragu, ya kwashe ya kai su zaman talala.


Can za ku bauta wa gumaka na itace, da na duwatsu, aikin hannuwan mutum, waɗanda ba su gani, ko ji, ko ci, ko sansana.


Waɗanda ba a kashe ba kuwa ya kwashe su, ya kai Babila, suka zama bayinsa da na 'ya'yansa maza har zuwa kahuwar mulkin Farisa,


Sai Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya hauro ya kara da shi. Ya kama shi, ya ɗaure shi da sarƙoƙi, ya kai shi Babila.


Don haka Ubangiji ya bashe su ga Sarkin Kaldiyawa wanda ya karkashe samarinsu da takobi a Haikali, bai yi juyayin saurayi, ko budurwa, ko tsoho, ko gajiyayye ba. Allah ya bashe su duka a hannunsa.


Saboda haka Ubangiji ya sa sarakunan yaƙi na Sarkin Assuriya su kamo Manassa da ƙugiyoyi, su ɗaure shi da sarƙoƙin tagulla, su kai shi Babila.


“Ubangiji zai warwatsa ku cikin dukan al'ummai daga wannan bangon duniya zuwa wancan. Can za ku bauta wa gumakan itace da na dutse waɗanda ku da kakanninku ba ku san su ba.


“Ya ku, mutanen Isra'ila, ni Ubangiji Allah, na ce, bari kowa ya tafi ya bauta wa gunkinsa daga yanzu zuwa gaba, tun da yake ba za ku kasa kunne gare ni ba, amma kada ku ɓata sunana mai tsarki da hadayunku da gumakanku.


Shi wanda muke dogara gare shi, Wato zaɓaɓɓe na Ubangiji, ya auka cikin raminsu, Shi wanda muka ce, “A ƙarƙashin inuwarsa ne za mu zauna a cikin sauran al'umma.”


Waɗansu daga cikin zuriyarka ta kanka, za a tafi da su a maishe su babani domin su yi hidima a fādar Sarkin Babila.’ ”


Kun ga abubuwan da suke da su masu banƙyama, wato gumakansu na itace, da na dutse, da na azurfa, da na zinariya.


Jama'ar ƙasa kuwa suka ɗauki Yehowahaz ɗan Yosiya suka naɗa shi sarki. Ya gaji tsohonsa a Urushalima.


Zan sa ku bauta wa abokan gābanku a ƙasar da ba ku sani ba, gama fushina ya kama kamar wuta, zai yi ta ci har abada.”


A watan goma a na shekara ta tara ta sarautar sarki Zadikiya, Sarkin Yahuza, sai Nebukadnezzar Sarkin Babila, da dukan sojojinsa suka zo, suka kewaye Urushalima da yaƙi.


‘Zan fitar da ku daga cikin birnin, in bashe ku a hannun baƙi, zan hukunta ku.


Ubangiji zai warwatsa ku cikin al'ummai. Za ku ragu kaɗan daga cikin al'ummai inda Ubangiji ya warwatsa ku.


Amma idan kuka ci gaba da aikata mugunta, za a shafe ku, ku da sarkinku.”


Sarkin Babila kuwa ya kashe su a can. Haka aka kai mutanen Yahuza zuwa zaman talala.


Domin haka, ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, zan ciyar da mutanen nan da abinci mai ɗaci, in shayar da su da ruwan dafi.


Ƙofofinta sun nutse ƙasa, Ya lalatar, ya kakkarya ƙyamarenta, An kai sarkinta da mahukuntanta cikin al'ummai, Inda ba a bin dokokin annabawanta, Ba su kuma samun wahayi daga wurin Ubangiji.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ