‘Ga shi, ku masu rainako, Za ku ruɗe don mamaki, ku shuɗe! Domin zan yi wani aiki a zamaninku, Aikin da ba yadda za a yi ku gaskata, Ko da wani ya gaya muku.’ ”
Da tsakar rana za ku riƙa lalubawa kamar makaho, ba za ku yi arziki cikin ayyukanku ba. Za a riƙa zaluntarku, ana yi muku ƙwace kullum, ba wanda zai cece ku.
“Sa'ad da duk waɗannan abubuwa suka same ku, wato albarka da la'ana waɗanda na sa a gabanku, in kun tuna da su a zuciyarku a duk inda kuke cikin al'ummai inda Ubangiji Allahnku ya kora ku,