Kun yi shuka da yawa, kun girbe kaɗan. Kun ci, amma ba ku ƙoshi ba. Kun sha ruwa, amma bai kashe muku ƙishi ba. Kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi. Wanda yake karɓar albashi kuwa, sai ka ce yana sawa a huɗajjen aljihu.”
Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.
Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.