Idan ba za ku kasa kunne ba, idan ba za ku sa a zuciyarku ku girmama sunana ba, to, zan aukar muku da la'ana, zan la'antar da albarkunku. Koyanzu ma na riga na la'antar da su domin ba ku riƙe umarnina a zuciyarku ba, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
Ubangiji ba zai yarda da mugayen ayyukanku ba, da ƙazantarku da kuka aikata, don haka ƙasarku a yau ta zama kufai ba mai zama a cikinta. Ta zama abin ƙyama da la'ana.
Idan na tafi cikin saura, Sai in ga waɗanda aka kashe da takobi! Idan kuma na shiga birni, Sai in ga waɗanda suke ta fama da yunwa! Gama annabi da firist, sai harkarsu suke ta yi a ƙasar, Amma ba su san abin da suke yi ba.’ ”
Urushalima wadda take cike da mutane a dā, Yanzu tana zaman kaɗaici! Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu, Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai! Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna, Ta zama mai biyan gandu!
Ta ce, “Na rantse da Ubangiji Allahnka, ba ni da abinci, sai dai ɗan farin da ya ragu a tukunya, da ɗan man da yake cikin kurtu. Ga shi, ina tattara itacen don in je in shirya shi domin ni da ɗana, mu ci. Shi ke nan, ba sauran wani abu kuma, sai mutuwa.”
Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”
domin kada ya ba wani daga cikinsu naman 'ya'yansa wanda yake ci, gama ba abin da ya rage masa saboda irin tsananin kewayewar garuruwanku da yaƙi wanda abokan gabanku suka kawo muku.
Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Zan aika da littafin a gidan ɓarawo da gidan mai rantsuwa da sunana a kan ƙarya. Littafin zai zauna a gidansa, ya ƙone gidan, da katakan, da duwatsun.’ ”