M.Sh 27:14 - Littafi Mai Tsarki14 Sa'an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra'ilawa: အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Lawiyawa za su karanta wa dukan mutanen Isra’ila da babbar murya su ce, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai Isra'ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama'ar Isra'ila albarka.