Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 27:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Waɗannan za su tsaya a bisa kan Dutsen Ebal don su la'anta, wato kabilar Ra'ubainu, da ta Gad, da ta Ashiru, da ta Zabaluna, da ta Dan, da ta Naftali.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 27:13
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da kuka haye Urdun ɗin sai ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal bisa ga umarnin da na yi muku yau. Ku yi musu shafe da farar ƙasa.


Sai Isra'ilawa duka, baƙi da haifaffun gida, tare da dattawansu da shugabanninsu, da alƙalansu, suka tsaya daura da akwatin alkawari, suna fuskantar firistoci, wato Lawiyawa, waɗanda suka ɗauki akwatin alkawari na Ubangiji. Rabin mutanen suka tsaya a gaban Dutsen Gerizim, rabinsu kuma suka tsaya a gaban Dutsen Ebal kamar yadda Musa, bawan Ubangiji, ya riga ya umarta, cewa su sa wa jama'ar Isra'ila albarka.


Sa'ad da Ubangiji Allahnku ya kai ku cikin ƙasar da za ku shiga ku mallake ta, sai ku ɗibiya albarkar a Dutsen Gerizim, ku ɗibiya la'anar kuma a Dutsen Ebal.


Sai Lai'atu ta ce, “Allah ya wadata ni da kyakkyawar baiwa, yanzu mijina zai darajanta ni, domin na haifa masa 'ya'ya maza shida,” ta raɗa masa suna Zabaluna.


Lai'atu fa ta yi ciki ta haifi ɗa, ta raɗa masa suna Ra'ubainu, gama ta ce, “Saboda Ubangiji ya dubi wahalata, hakika, yanzu mijina zai ƙaunace ni.”


“Sa'ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama'a albarka, wato kabilar Saminu, da ta Lawi, da ta Yahuza, da ta Issaka, da ta Yusufu, da ta Biliyaminu.


Sa'an nan Lawiyawa za su ta da murya, su ce wa dukan Isra'ilawa:


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ