Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 26:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Masarawa suka wulakanta mu, suka tsananta mana, suka bautar da mu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Amma Masarawa suka wulaƙanta mu suka sa muka sha wahala, suna sa mu aikin dole.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 26:6
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Suka kuwa naɗa musu shugabannin aikin gandu domin su wahalshe su da mawuyacin aiki. Aka sa su su gina wa Fir'auna biranen ajiya, wato Fitom da Ramases.


Suka baƙanta musu rai da aiki mai tsanani na kwaɓa, da yin tubali, da kowane irin aiki a saura. A cikin ayyukansu duka suka tsananta musu.


Amma ku, Ubangiji ya fisshe ku daga gidan bauta mai zafi, wato Masar, don ku zama jama'arsa ta musamman kamar yadda kuke a yau.


Gama tun da na tafi wurin Fir'auna, na yi masa magana da sunanka, ya mugunta wa wannan jama'a, kai kuwa ba ka ceci jama'arka ba ko kaɗan!”


Manyan Isra'ilawa suka ga lalle sun shiga uku, da yake aka ce dole su cika yawan tubali da aka yanka musu kowace rana.


Ku sa mutanen su yi aiki mai tsanani har da ba za su sami damar kasa kunne ga maganganun ƙarya ba.”


Fir'auna kuwa ya umarci dukan mutanensa ya ce, “Duk jaririn da aka haifa wa Ibraniyawa, sai ku jefa shi cikin Kogin Nilu, amma idan jaririya ce, ku bar ta da rai.”


“Sa'ad da kuke yi wa matan Ibraniyawa hidimarku ta ungozomai, in kuka gan su durƙushe, in jariri ne suka haifa, sai ku yi masa sanadin mutuwa, in kuma jaririya ce, ku bar ta da rai.”


A wannan lokaci kuwa aka yi wani sabon sarki a Masar wanda bai san Yusufu ba.


Amma muka yi kuka ga Ubangiji Allah na kakanninmu. Ubangiji kuwa ya ji kukanmu, ya ga azabarmu, da wahalarmu, da zaluncin da ake yi mana.


yadda kakanninmu suka gangara zuwa Masar, suka zauna a can da daɗewa, da yadda Masarawa suka wahalshe mu, mu da kakanninmu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ