M.Sh 24:15 - Littafi Mai Tsarki15 Sai ku biya shi hakkinsa a ranar da ya yi aikin, kafin faɗuwar rana, gama shi matalauci ne, zuciyarsa tana kan abin hakkinsa, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har ya zama laifi a gare ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Ku biya kuɗin aikinsa kowace rana kafin fāɗuwar rana, domin shi matalauci ne, yana kuma sa rai a kan wannan hakkin ne, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har yă zama laifi a gare ku. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”