Daga baya kuma ɗan'uwansa ya fito, hannunsa na riƙe da diddigen Isuwa, saboda haka aka raɗa masa suna Yakubu. Ishaku yana da shekara sittin sa'ad da ya haife su.
Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.
Bayan da aka gama waɗannan abubuwa, sai shugabanni suka zo wurina, suka ce, “Mutanen Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa ba su keɓe kansu daga ƙazantar mutanen ƙasar ba, wato su Kan'aniyawa, da Hittiyawa, da Ferizziyawa, da Yebusiyawa, da Ammonawa, da Mowabawa, da Masarawa, da Amoriyawa.