Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




M.Sh 23:23 - Littafi Mai Tsarki

23 Sai ku cika duk abin da kuka faɗa da bakinku, gama da yardarku ne kuka yi wa Ubangiji Allahnku wa'adi wanda kuka alkawarta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

23 Duk abin da ya fita daga bakinku, sai ku lura ku cika shi, kamar yadda kuka yarda da kanku, kuka yi alkawarin ga Ubangiji Allahnku da bakinku.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




M.Sh 23:23
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ka yi tunani a hankali kafin ka yi wa'adi za ka miƙa wa Allah wani abu, mai yiwuwa ne ka yi da na sani nan gaba.


Amma kada ka yardar musu, don fiye da mutum arba'in daga cikinsu suna fakonsa, sun kuma yi rantsuwa a kan ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe shi. Yanzu kuwa a shirye suke, yardarka kawai suka jira.”


Da gari ya waye, Yahudawa suka gama baki suka yi rantsuwa, cewa ba za su ci ba, ba za su sha ba, sai sun kashe Bulus.


A taron dukan jama'arka, A shirayun Haikalinka, A Urushalima, zan ba ka abin da na alkawarta. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!


A ran nan kuwa Isra'ilawa sun sha wahala, gama Saul ya yi rantsuwa mai ƙarfi ya ce, “La'ananne ne mutumin da ya ci abinci kafin faɗuwar rana tun ban ɗauko fansa a kan abokan gābana ba.” Don haka ba mutumin da ya ɗanɗana abinci.


Ta yi wa'adi, ta ce, “Ya Ubangiji Mai Runduna, idan lalle ka dube ni, ni baiwarka, ka tuna da ni, ba ka manta da ni baiwarka ba, amma ka ba ni ɗa, ni ma sai in ba da shi ga Ubangiji dukan kwanakinsa, aska kuwa ba za ta taɓa kansa ba.”


Idan mutum ya yi wa'adi ga Ubangiji, ko kuwa ya rantse zai yi wani abu, ko kuwa ba zai yi wani abu ba, to, kada ya warware maganarsa, amma sai ya aikata abin da bakinsa ya hurta.


Sa'ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, 'yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa'adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.”


“Har wa yau dai kun ji an faɗa wa mutanen dā, ‘Kada ka rantse a kan ƙarya, sai dai ka cika wa'adin da ka ɗaukar wa Ubangiji.’


Idan kun nisanci yin wa'adi, ba zai zama zunubi gare ku ba.


“Sa'ad da kuka shiga gonar inabin maƙwabcinku, kuna iya cin 'ya'yan inabin, har ku ƙoshi yadda kuke so, amma kada ku sa wani a jakarku.


Za mu aikata dukan abin da muka faɗa. Za mu miƙa wa gunkiyan nan, wato sarauniyar sama, hadayu, da hadayu na sha kamar yadda kakanninmu, da shugabanninmu suka yi a garuruwan Yahuza, da kan titunan Urushalima. A lokacin kuwa muna da abinci a wadace, muka arzuta, ba wata wahala.


waɗannan ka'idodi domin Isra'ilawa. Idan an ba da mutum ga Ubangiji don cikar babban wa'adi za a iya fansarsa ta wurin biya waɗannan kuɗi.


Amma Isra'ilawa ba su kashe su ba, domin shugabannin jama'a sun rantse musu da sunan Ubangiji Allah na Isra'ila. Dukan jama'a kuwa suka yi gunaguni a kan shugabannin.


Bari ku miƙa wa Allah hadayarku ta godiya, Ku ba Mai Iko Dukka, dukan hadayun da kuka alkawarta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ